9 wanda ya gayyato ku duka biyu kuma yă zo ya ce maka, ‘Ba mutumin nan wuri.’ Sa'an nan a kunyace ka koma mazauni mafi ƙasƙanci.
10 Amma in an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi ƙasƙanci, don in mai gayyar ya zo, sai ya ce maka, ‘Aboki, hawo nan mana.’ Za ka sami girma ke nan a gaban dukan waɗanda kuke zaune tare.
11 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”
12 Ya kuma ce da mai gayyar, “In za ka kira mutum cin abinci ko biki, kada ka riƙa kiran abokanka kawai, ko 'yan'uwanka, ko danginka ko maƙwabtanka masu arziki, kada su ma su gayyace ka, su sāka maka.
13 Amma in za ka kira biki, sai ka gayyayo gajiyayyu, da musakai, da guragu, da makafi,
14 za ka kuwa sami albarka, da yake ba su da hanyar sāka maka. Sai kuwa a sāka maka ranar tashin masu adalci.”
15 Da jin haka, sai ɗaya daga cikin abokan cinsa ya ce masa, “Albarka tā tabbata ga wanda zai ci abinci a Mulkin Allah.”