5 Sai ya kira mabartan maigidansa da ɗaya ɗaya, ya ce wa na farko, ‘Nawa maigida yake bin ka?’
6 Ya ce, ‘Garwa ɗari ta mai.’ Sai ya ce masa, ‘Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubutu hamsin,’
7 Ya kuma ce wa wani, ‘Kai fa, nawa ake binka?’ Sai ya ce, ‘Buhu ɗari na alkama.’ Ya ce masa, ‘Ga takardarka, ka rubuta tamanin.’
8 Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo.
9 Ina gaya muku, ku yi abokai ta dukiya, ko da yake aba ce wadda take iya aikata mugunta, don sa'ad da ta ƙare su karɓe ku a gidaje masu dawwama.
10 “Wanda yake da aminci a ƙaramin abu, mai aminci ne a babban abu. Wanda yake marar gaskiya a ƙaramin abu, marar gaskiya ne a babban abu.
11 Idan fa ba ku yi aminci da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya?