22 Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Har yanzu abu guda ne kawai ya rage maka, ka sayar da duk mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”
23 Da jin haka, sai ya yi baƙin ciki gaya, don shi mai arziki ne da gaske.
24 Yesu kuwa da ya gan shi haka, ya ce, “Kai! Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!
25 Ai, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”
26 Waɗanda suka ji wannan magana suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”
27 Amma Yesu ya ce, “Abin da ya fi ƙarfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”
28 Sai Bitrus ya ce, “To, ai, ga shi, mun bar mallakarmu, mun bi ka.”