9 Sai kuma ya ba da misalin nan ga waɗansu masu amince wa kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, ya ce,
10 “Waɗansu mutum biyu suka shiga Haikali yin addu'a, ɗaya Bafarisiye, ɗaya kuma mai karɓar haraji.
11 Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu'a ga kansa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan.
12 Duk mako ina azumi sau biyu. Kome na samu nakan fitar da zakka.’
13 Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!’
14 Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”
15 Waɗansu suka kawo masa 'yan yaransu domin ya taɓa su. Ganin haka sai almajiransa suka kwaɓe su.