43 Don lokaci zai auko muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya, su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe,
44 su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan'uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”
45 Sai ya shiga Haikali, ya fara korar masu sayarwa,
46 ya ce musu, “Ai, a rubuce yake cewa, ‘Ɗakina zai kasance ɗakin addu'a.’ Amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”
47 Kowace rana ya yi ta koyarwa a Haikali. Amma manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka nema su hallaka shi.
48 Suka kuwa rasa abin da za su yi, saboda maganarsa ta ɗauke wa duk jama'a hankali.