38 Nan take ita ma ta zo, ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi maganar ɗan yaron nan ga dukan masu sauraron fansar Urushalima.
39 Bayan sun ƙare kome da kome bisa ga Shari'ar Ubangiji, sai suka koma ƙasar Galili suka tafi garinsu Nazarat.
40 Ɗan yaron kuwa ya girma, ya kawo ƙarfi, yana mai matuƙar hikima. Alherin Allah kuwa yana tare da shi.
41 To, iyayensa sukan je Urushalima kowace shekara a lokacin Idin Ƙetarewa.
42 Da ya shekara goma sha biyu, sai suka tafi tare da shi bisa ga al'adarsu a lokacin Idi.
43 Da aka gama idin kuma, suna cikin komowa, sai yaron, wato Yesu, ya tsaya a Urushalima, ba da sanin iyayensa ba.
44 Su kuwa suka yi ta tafiya yini guda, suna zaton yana cikin ayari. Sai suka yi ta cigiyarsa cikin 'yan'uwansu da idon sani.