3 Sai ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku gaya mini,
4 baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?”
5 Sai suka yi muhawwara da juna suka ce, “In mun ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
6 In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ sai duk jama'a su jajjefe mu, don sun tabbata Yahaya annabi ne.”
7 Sai suka amsa masa, suka ce, ba su san daga inda take ba.
8 Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”
9 Sai ya shiga ba jama'a misalin nan, ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya ba waɗansu manoma ijararta, ya kuma tafi wata ƙasa, ya daɗe.