27 A sa'an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa.
28 Sa'ad da waɗannan al'amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, domin fansarku ta yi kusa.”
29 Sai ya ba su wani misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa,
30 da zarar sun fara toho, kuna gani, ku da kanku kun san damuna ta yi kusa ke nan.
31 Haka kuma sa'ad da kuka ga waɗannan al'amura suna aukuwa, ku sani Mulkin Allah ya gabato.
32 Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba, sai duk abubuwan nan sun auku.
33 Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”