39 Sai ya fita ya tafi Dutsen Zaitun, kamar yadda ya saba. Almajiransa kuwa suka bi shi.
40 Da ya iso wurin, ya ce musu, “Ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji.”
41 Sai ya ɗan rabu da su misalin nisan jifa, ya durƙusa, ya yi addu'a.
42 Ya ce, “Ya Uba, in dai ka yarda, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi” [
43 Sai wani mala'ika ya bayyana a gare shi daga Sama, yana ƙarfafa shi.
44 Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu'a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.]
45 Da ya tashi daga addu'a, ya koma wurin almajiran, ya tarar suna barci saboda baƙin ciki.