32 Waɗansu mutum biyu kuma masu laifi, aka kai su a kashe su tare da shi.
33 Da suka isa wurin da ake ce da shi Ƙoƙwan Kai, nan suka gicciye shi, da kuma masu laifin nan, ɗaya a damansa, ɗaya a hagun.
34 Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri'a a kansu.
35 Mutane da suke tsaitsaye, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa ba'a, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah zaɓaɓɓensa!”
36 Soja kuma suka yi masa ba'a, suka matso, suka miƙa masa ruwan tsami,
37 suna cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ka cece kanka mana!”
38 Sama da shi kuma aka yi wani rubutu cewa, “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”