24 Waɗansunsu da suke tare da mu kuma, suka je kabarin, suka tarar kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.”
25 Sai Yesu ya ce musu, “Ya ku mutane marasa fahimta, masu nauyin gaskata duk abin da annabawa suka faɗa!
26 Ashe, ba wajibi ne Almasihu ya sha wuyar waɗannan abubuwa ba, ya kuma shiga ɗaukakarsa?”
27 Sai ya fara ta kan littattafan Musa da na dukan annabawa, ya yi ta bayyana musu abubuwan da suka shafe shi a dukan Littattafai.
28 Sai suka kusato ƙauyen da za su. Ya yi kamar zai ci gaba,
29 suka matsa masa suka ce, “Sauka a wurinmu, ai, magariba ta doso, rana duk ta tafi.” Sai ya sauka a wurinsu.
30 Sa'ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su.