17 Aka miƙa masa Littafin Annabi Ishaya, ya buɗe littafin, ya sami inda aka rubuta cewa,
18 “Ruhun Ubangiji yana tare da ni,Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara.Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru,In kuma buɗe wa makafi ido,In kuma 'yanta waɗanda suke a danne,
19 In yi shelar zamanin samun karɓuwa ga Ubangiji.”
20 Ya rufe littafin ya mayar wa mai hidima, ya zauna. Duk waɗanda suke cikin majami'a suka zuba masa ido.
21 Sai ya fara ce musu, “Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.”
22 Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”
23 Yesu ya ce musu, “Lalle za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka.’ Za ku kuma ce mini, ‘Duk abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, ka yi a nan garinku mana.’ ”