26 Duk da haka ba a aiki Iliya gun ko ɗaya daga cikinsu ba, sai ga wata mace kaɗai a Zarifat ta ƙasar Sidon wadda mijinta ya mutu.
27 A zamanin Annabi Elisha kuma akwai kutare da yawa a Isra'ila, ba kuwa ɗayansu da aka tsarkake sai Na'aman, mutumin Suriya, kaɗai.”
28 Da suka ji haka, duk waɗanda suke a majami'a suka husata ƙwarai.
29 Sai suka tashi suka fitar da shi bayan gari, har suka kai shi goshin dutsen da aka gina garinsu a kai, don su jefa shi ƙasa.
30 Amma ya ratsa ta tsakiyarsu, ya yi tafiyarsa.
31 Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a ƙasar Galili, yana koya musu ran Asabar.
32 Suka yi mamakin koyarwarsa domin magana tasa da hakikancewa take.