4 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”
5 Sai Iblis ya kai shi wani wuri a bisa, ya nunnuna masa dukkan mulkokin duniya a ƙyiftawar ido.
6 Iblis ya ce masa, “Kai zan bai wa ikon duk waɗannan, da ɗaukakarsu, don ni aka danƙa wa, nakan kuma bayar ga duk wanda na ga dama.
7 In kuwa za ka yi mini sujada, duk su zama naka.”
8 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada,Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”
9 Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan,
10 don a rubuce yake cewa,‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai, su kiyaye ka,’