7 In kuwa za ka yi mini sujada, duk su zama naka.”
8 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada,Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”
9 Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan,
10 don a rubuce yake cewa,‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai, su kiyaye ka,’
11 da kuma‘Za su tallafe ka,Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”
12 Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai kuwa an ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”
13 Bayan da Iblis ya gama irin dukan gwaje-gwajensa, ya rabu da shi ɗan lokaci tukuna.