6 Da suka yi haka kuwa, suka kamo kifi jingim, har ma tarunansu suka fara kecewa.
7 Sai suka yafato abokan aikinsu a ɗaya jirgin su zo su taimake su. Suka kuwa zo, suka ciccika jiragen nan duka biyu kamar sa nutse.
8 Da Bitrus ya ga haka, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce. “Ya Ubangiji, wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi.”
9 Domin shi da waɗanda suke tare da shi duka, mamaki ya kama su saboda kifin nan da suka janyo,
10 haka ma Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi, abokan sabgar Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.”
11 Da suka kawo jiragensu gaci, suka bar kome duka suka bi shi.
12 Wata rana Yesu na ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa ya zo. Da ya ga Yesu ya fāɗi a gabansa, ya roƙe shi ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda kana da ikon tsarkake ni.”