2 ya kuma aike su su yi wa'azin Mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.
3 Ya kuma ce musu, “Kada ku ɗauki wani guzuri a tafiyarku, ko sanda, ko burgami, ko gurasa, ko kuɗi. Kada kuma ku ɗauki taguwa biyu.
4 Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.
5 Duk waɗanda ba su yi na'am da ku ba, in za ku bar garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”
6 Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna yin bishara, suna warkarwa a ko'ina.
7 To, sarki Hirudus ya ji duk abin da ake yi, ya kuwa damu ƙwarai, don waɗansu suna cewa Yahaya ne aka tasa daga matattu.
8 Waɗansu kuwa suka ce wai Iliya ne ya bayyana. Waɗansu kuma suka ce ɗaya daga annabawan dā ne ya tashi.