1 Farkon bisharar Yesu Almasihu, Ɗan Allah, ke nan.
2 Yadda yake a rubuce a littafin Annabi Ishaya cewa,“Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,Wanda zai shirya maka hanya.
3 Muryar mai kira a jeji tana cewa,Ku shirya wa Ubangiji tarfarki,Ku miƙe hanyoyinsa.”
4 Yahaya Maibaftisma ya bayyana a jeji, yana wa'azi mutane su tuba a yi musu baftisma domin a gafarta musu zunubansu.