27 Yesu ya dube su, ya ce, “Ga mutane kam ba mai yiwuwa ba ne, amma fa ba ga Allah ba. Domin kowane abu mai yiwuwa ne a gun Allah.”
28 Sai Bitrus ya fara ce masa, “To, ai, ga shi, mu mun bar kome, mun bi ka.”
29 Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko 'yan'uwansa mata, ko 'yan'uwansa maza, ko uwa tasa, ko ubansa, ko 'ya'yansa, ko gonakinsa, sabili da ni da kuma bishara,
30 sa'an nan ya kasa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, na gidaje, da 'yan'uwa mata, da 'yan'uwa maza, da iyaye mata, da 'ya'ya, da gonaki, amma game da tsanani, a lahira kuma ya sami rai madawwami.
31 Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”
32 Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na tafe gabansu, sai suka yi mamaki, mutanen da suke biye kuma suka tsorata. Ya sāke keɓe sha biyun nan, ya fara shaida musu abin da zai same shi.
33 Ya ce, “Ga shi, za mu Urushalima, za a ba da Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, su bāshe shi ga al'ummai.