32 Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na tafe gabansu, sai suka yi mamaki, mutanen da suke biye kuma suka tsorata. Ya sāke keɓe sha biyun nan, ya fara shaida musu abin da zai same shi.
33 Ya ce, “Ga shi, za mu Urushalima, za a ba da Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, su bāshe shi ga al'ummai.
34 Za su yi masa ba'a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi.”
35 Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka kusato shi, suka ce masa, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙe ka.”
36 Sai ya ce musu, “Me kuke so in yi muku?”
37 Suka ce masa, “Ka yardar mana, ranar ɗaukakarka, mu zauna ɗaya a damanka, ɗaya a hagun.”
38 Amma Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya sha da ƙoƙon da ni zan sha? Ko kwa iya a yi muku baftisma da baftismar da za a yi mini?”