9 Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”
10 A cikin gida kuma sai almajiransa suka sāke tambayarsa wannan magana.
11 Sai ya ce musu, “Kowa ya saki mata tasa, ya auri wata, zina yake yi da ta biyun.
12 In kuma matar ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”
13 Suna kawo masa waɗansu yara ƙanana domin ya taɓa su, sai almajiransa suka kwaɓe su.
14 Da Yesu ya ga haka, sai ya ji haushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne.
15 Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na'am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”