1 Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.
2 Da kakar inabin ta yi, sai ya aiki wani bawansa wurin manoman nan ya karɓo masa gallar garkar.
3 Manoman kuwa suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hanu banza.
4 Sai ya sāke aika musu wani bawa. Shi kuma suka yi masa rotsi, suka wulakanta shi.
5 Ya sāke aiken wani, shi kam, sai suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da waɗansu da yawa, ana dūkan waɗansu, ana kashe waɗansu.