18 Sai Sadukiyawa (su da suke cewa, wai ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka tambaye shi suka ce,
19 “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar mata tasa ba ɗa, sai lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.
20 To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure, ya mutu bai bar baya ba.
21 Na biyun kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba ɗa. Na ukun ma haka.
22 Haka dai duk bakwai ɗin, ba wanda ya bar ɗa. Daga ƙarshe kuma ita matar ta mutu.
23 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”
24 Sai Yesu ya ce musu, “Ba saboda wannan ne ya sa kuka ɓata ba? Wato don ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba.