35 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya faɗi ƙasa, ya yi addu'a ko ya yiwu a ɗauke masa wannan lokaci.
36 Sa'an nan ya ce, “Ya Abba, Uba, kowane abu mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”
37 Ya komo ya samu suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Bitrus, barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a faɗake ko da sa'a ɗaya ba?
38 Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”
39 Sai ya sāke komawa, ya yi addu'a, yana maimaita maganar dā.
40 Har wa yau kuma ya sāke dawowa, ya samu suna barci, don duk barci ya cika musu ido ƙwarai, sun kuwa rasa abin da za su ce masa.
41 Ya sāke komowa zuwa na uku, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka. Lokaci ya yi. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi.