62 Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum zaune dama ga Mai Iko, yana kuma zuwa cikin gajimare.”
63 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Wace shaida kuma za mu nema?
64 Kun dai ji saɓon da ya yi! Me kuka gani?” Duk suka yanke masa shari'a a kan ya cancanci kisa.
65 Waɗansu ma suka fara tattofa masa yau, suka ɗaure masa idanu, suka bubbuge shi, suna ce masa, “Yi annabci!” Dogaran Haikali kuma suka yi ta marinsa.
66 Bitrus kuwa na ƙasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo.
67 Da ta ga Bitrus na jin wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Banazaren nan Yesu!”
68 Amma ya musa ya ce, “Ni ban ma san abin da kike faɗa ba, balle in fahimta.” Sai ya fito zaure. Zakara kuwa ya yi cara.