15 Bilatus kuwa da yake yana son ƙayatar da jama'a, ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, ya ba da shi a gicciye shi.
16 Sai soja suka tafi da shi cikin fada, wato fadar mai mulkin, suka tara dukkan rundunar soja.
17 Suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura, suka kuma yi wani kambi na ƙaya, suka sa masa a kā.
18 Sai suka fara gaishe shi, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!”
19 Suka riƙa ƙwala masa sanda a ka, suna tattofa masa yau, sa'an nan suka durƙusa, wai suna masa ladabi.
20 Da suka gama yi masa ba'a haka, suka yaye masa alkyabba mai ruwan jar garura, suka sa masa nasa tufafi, suka kai shi waje don su gicciye shi.
21 Sai ga wani mai wucewa, wai shi Saminu Bakurane, uban Iskandari da Rufas, yana zuwa daga ƙauye. Suka fa tilasta masa ya ɗauki gicciyen Yesu.