21 Sai ga wani mai wucewa, wai shi Saminu Bakurane, uban Iskandari da Rufas, yana zuwa daga ƙauye. Suka fa tilasta masa ya ɗauki gicciyen Yesu.
22 Suka kai Yesu wani wuri wai shi Golgota, wato wurin ƙoƙon kai.
23 Suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, amma ya ƙi sha.
24 Sa'an nan suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu, suna kuri'a a kansu, su ga abin da kowa zai samu.
25 Da ƙarfe tara na safe suka gicciye shi.
26 Aka kuma rubuta sanarwar laifinsa sama da shi, wato “Sarkin Yahudawa.”
27 Suka kuma gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya dama da shi, ɗaya kuma a hagun. [