3 Sai manyan firistoci suka yi ta kai ƙararsa a kan abubuwa da yawa.
4 Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba ka da wata amsa? Dubi yawan maganganu da suke ba da shaida a kanka!”
5 Yesu dai har yanzu bai yi wata magana ba, har Bilatus ya yi mamaki.
6 To, a lokacin idi kuwa Bilatus ya saba sakar musu kowane ɗan sarƙa guda da suka roƙa.
7 Akwai wani wai shi Barabbas da yake ɗaure, tare da waɗansu 'yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin tawayen.
8 Jama'a fa suka matso, suka fara roƙon Bilatus ya yi musu abin da ya saba yi.
9 Sai ya amsa musu, ya ce, “Wato kuna so ne in sakar muku Sarkin Yahudawa?”