1 Sai ya sāke shiga majami'a. Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu.
2 Sai suka yi haƙwansa su ga ko zai warkar da shi ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa.
3 Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Fito nan fili.”
4 Ya ce musu, “Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko kuwa mugunta? A ceci rai, ko kuwa a kashe shi?” Amma sai suka yi shiru.
5 Da ya duddube su da fushi, yana baƙin ciki da taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
6 Da Farisiyawa suka fita, nan da nan suka yi shawara da mutanen Hirudus a kansa, yadda za su hallaka shi.