10 Da suka kaɗaita, masu binsa da su sha biyun nan suka tambaye shi ma'anar misalan.
11 Sai ya ce musu, “Ku kam, an yardar muku ku san asirin Mulkin Allah, amma ga waɗanda ba sa cikinku, kome sai a cikin misali,
12 don gani da ido kam, su gani, amma ba da zuci ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba, wai don kada su juyo a yafe musu.”
13 Ya ce musu, “Ashe, ba ku fahimci wannan misali ba? Ƙaƙa za ku fahimci sauran ke nan?
14 Mai shukan nan fa Maganar Allah yake shukawa.
15 Waɗanda suka fāda a hanya kuwa, su ne kwatancin waɗanda aka shuka Maganar a zuciya tasu. Da zarar sun ji, nan da nan sai Shaiɗan ya zo ya ɗauke Maganar da aka shuka a zuciya tasu.
16 Haka kuma waɗanda aka shuka a wuri mai duwatsu, su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar sai su karɓa da farin ciki.