22 Da 'yar Hirudiya ta shigo ta yi rawa, sai ta gamshi Hirudus da baƙinsa. Sai fa sarki ya ce wa yarinyar, “Roƙe ni kome, sai in ba ki.”
23 Ya kuma rantse mata, ya ce, “Kome kika roƙe ni zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”
24 Ta fita, ta ce wa uwa tata, “Me zan roƙa?” Uwar ta ce, “Kan Yahaya Maibaftisma.”
25 Nan da nan sai ta shigo wurin sarki da gaggawa, ta roƙe shi, ta ce, “Ina so yanzu yanzu ka ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi.”
26 Sai sarki ya yi baƙin ciki gaya, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ba ya so ya hana ta.
27 Nan take sai sarki ya aiki dogari, ya yi umarni a kawo kan Yahaya. Ya tafi ya fille wa Yahaya kai a kurkuku,
28 ya kawo kan a cikin akushi, ya ba yarinyar, yarinyar kuwa to ba uwa tata.