38 Ya ce musu, “Gurasa nawa gare ku? Ku je ku dubo.” Da suka binciko suka ce, “Ai, biyar ne, da kifi biyu.”
39 Sa'an nan ya yi umarni dukkansu su zazzauna ƙungiya ƙungiya a ɗanyar ciyawa.
40 Haka suka zauna jeri jeri, waɗansu ɗari ɗari, waɗansu hamsin hamsin.
41 Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu.
42 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi,
43 har suka ɗauki kwando goma sha biyu cike da gutsattsarin gurasar da na kifin.
44 Waɗanda suka ci gurasan nan kuwa maza dubu biyar ne.