6 Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu.Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.
7 Sai ya kira goma sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu.
8 Ya umarce su kada su ɗauki guzuri don tafiyar, ko gurasa, ko burgami, ko kuɗi ma a ɗamararsu, sai dai sanda kawai,
9 amma su sa takalmi, kada kuma su haɗa taguwa biyu.
10 Ya ce musu, “Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.
11 Duk inda aka ƙi yin na'am da ku, aka kuma ƙi sauraronku, in za ku tashi, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunka don shaida a kansu.”
12 Haka fa, suka fita, suna wa'azi mutane su tuba.