5 Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka tambaye shi, “Don me almajiranka ba sa bin al'adun shugabanni, sai su riƙa cin abinci da hannuwa marasa tsarki?”
6 Sai ya ce musu, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, munafukai! Yadda yake a rubuce cewa,‘Al'umman nan a baka kawai suke girmama ni,Amma a zuci nesa suke da ni.
7 A banza suke bauta mini,Domin ƙa'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’
8 Kuna yar da umarnin Allah, kuna riƙe da al'adun mutane.”
9 Sai ya ce musu, “Lalle kun iya yar da umarnin Allah don ku bi al'adunku!
10 Domin Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ da kuma, ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa, sai lalle a kashe shi.’
11 Amma ku kukan ce, ‘In mutum ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni ya zama Korban,” ’ (wato an sadaukar),