1 Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
2 To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya,
3 da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza,
4 da Saminu Bakan'ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.