11 Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma baƙunce shi har ku tashi.
12 In za ku shiga gidan ku ce, ‘Salama alaiku.’
13 In gidan na kirki ne, salamarku tă tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, tă komo muku.
14 Kowa kuma ya ƙi yin na'am da ku, ko kuwa ya ƙi sauraron maganarku, da fitarku gidan ko garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku.
15 Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari'a za a fi haƙurce wa ƙasar Saduma da ta Gwamrata a kan garin nan.”
16 “Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.
17 Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi muku bulala a majami'arsu.