35 Domin na zo ne in haɗa mutum da ubansa gāba, 'ya da uwatata, matar ɗa kuma da surukarta.
36 Zai zamana kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa.
37 Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.
38 Wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba.
39 Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, adana shi yake yi.”
40 “Wanda ya yi na'am da ku, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.
41 Wanda ya yi na'am da wani annabi domin shi annabi ne, zai sami ladar annabi. Wanda kuma ya yi na'am da adali domin shi adali ne, zai sami ladar adali.