4 da Saminu Bakan'ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.
5 Su sha biyun nan ne Yesu ya aika, ya yi musu umarni, ya ce, “Kada ku shiga ƙasar al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa.
6 Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama'ar Isra'ila,Irm
7 kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, ‘Mulkin Sama ya kusato.’
8 Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta.
9 Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurfa, ko na tagulla a ɗamararku,
10 kada kuma ku ɗauki burgami a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci hakkinsa.