12 Tun daga zamanin Yahaya Maibaftisma har ya zuwa yanzu, Mulkin Sama yana shan kutse, masu kutsawa kuwa sukan riske shi.
13 Domin dukan annabawa da Attaura sun yi annabci har ya zuwa kan Yahaya.
14 In kuma za ku karɓa, shi ne Iliya da dā ma zai zo.
15 Duk mai kunnen ji, yă ji.
16 “To, da me zan kwatanta zamanin nan? Kamar yara ne da suke zaune a kasuwa, suna kiran abokan wasansu, suna cewa,
17 ‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba,Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba!’
18 “Ga shi, Yahaya ya zo, ya ƙi ciye-ciye da shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da iska.’