25 A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.
26 Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.
27 Kowane abu Ubana ne ya mallakar mini. Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa.
28 Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku.
29 Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali'u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.
30 Domin bautata sassauƙa ce, kayana kuma marar nauyi ne.”