1 A lokacin nan a ran Asabar, Yesu yana ratsa gonakin alkama. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara zagar alkamar suna ci.
2 Amma da Farisiyawa suka ga haka, suka ce masa, “Ka ga! Almajiranka suna yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba.”
3 Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa'ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa?
4 Yadda ya shiga Ɗakin Allah ya ci keɓaɓɓiyar gurasar nan, wadda bai halatta ya ci ba, ko abokan tafiyarsa ma su ci ba, sai dai firistoci kaɗai?