32 Ita ce mafi ƙanƙanta a cikin ƙwayoyi, amma in ta girma, sai ta fi duk sauran ganyaye, har ta zama itace, har ma tsuntsaye su zo su yi sheƙarsu a rassanta.”
33 Ya kuma ba su wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar yisti yake, wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗe da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”
34 Yesu ya gaya wa taro duk waɗannan abubuwa da misalai. Ba ya faɗa musu kome sai da misali.
35 Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,“Zan yi magana da misalai,Zan sanar da abin da yake ɓoye tun farkon duniya.”
36 Sai ya bar taron, ya shiga gida. Almajiransa kuma suka zo gare shi, suka ce, “Ka fassara mana misalin nan na ciyawa a gonar.”
37 Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗan Mutum.
38 Gonar kuwa ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, su ne 'ya'yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, 'ya'yan Mugun ne.