43 Sa'an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”
44 “Mulkin Sama kamar dukiya yake da take binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana tsaka da murna tasa, sai ya je ya sayar da dukan mallaka tasa, ya sayi gonar.”
45 “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar attajiri yake, mai neman lu'ulu'u masu daraja.
46 Da ya sami lu'ulu'u ɗaya mai tamanin gaske, sai ya je ya sai da dukan mallaka tasa, ya saye shi.”
47 “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar taru yake da aka jefa a teku, ya kamo kifi iri iri.
48 Da ya cika, aka jawo shi gaci, aka zauna, aka tsince kyawawan kifi, aka zuba a goruna, munanan kuwa aka watsar.
49 Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala'iku za su fito, su ware mugaye daga masu adalci,