47 “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar taru yake da aka jefa a teku, ya kamo kifi iri iri.
48 Da ya cika, aka jawo shi gaci, aka zauna, aka tsince kyawawan kifi, aka zuba a goruna, munanan kuwa aka watsar.
49 Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala'iku za su fito, su ware mugaye daga masu adalci,
50 su jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora.”
51 “Kun fahimci duk wannan?” Suka ce masa, “I.”
52 Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”
53 Da Yesu ya gama waɗannan misalai, sai ya tashi daga nan.