49 Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala'iku za su fito, su ware mugaye daga masu adalci,
50 su jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora.”
51 “Kun fahimci duk wannan?” Suka ce masa, “I.”
52 Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”
53 Da Yesu ya gama waɗannan misalai, sai ya tashi daga nan.
54 Da ya zo garinsu, ya koya musu a majami'arsu, har suka yi mamaki, suka ce, “Daga ina mutumin nan ya sami wannan hikima haka, da kuma mu'ujizan nan?
55 Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba?