1 A lokacin nan sarki Hirudus ya ji labarin shaharar Yesu.
2 Sai ya ce wa barorinsa, “Wannan, ai, Yahaya Maibaftisma ne, shi aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”
3 Don dā ma Hirudus ya kama Yahaya ya ɗaure shi, ya sa shi kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗan'uwansa Filibus.
4 Don dā ma Yahaya ya ce masa bai halatta ya zauna da ita ba.
5 Ko da yake yana son kashe shi, yana jin tsoron jama'a, don sun ɗauka shi annabi ne.