32 Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.”
33 Sai almajiran suka ce masa, “Ina za mu samo gurasa a jeji haka da za ta isa ciyar da ƙasaitaccen taro haka?”
34 Yesu ya ce musu, “Gurasa nawa suke gare ku?” Suka ce, “Bakwai, da ƙananan kifaye kaɗan.”
35 Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa.
36 Da ya ɗauki gurasa bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma na, bai wa jama'a.
37 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai.
38 Waɗanda suka ci kuwa maza dubu huɗu ne, banda mata da yara.