13 Sa'an nan ne almajiran suka gane, ashe, zancen Yahaya Maibaftisma yake yi musu.
14 Da suka isa wurin taro, sai wani mutum ya zo gare shi, ya durƙusa a gabansa, ya ce,
15 “Ya Ubangiji, ka ji tausayin ɗana, yana farfaɗiya, yana shan wuya ƙwarai, sau da yawa yakan faɗa wuta da kuma ruwa.
16 Na kuwa kai shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”
17 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.”
18 Sai Yesu ya tsawata masa, aljanin kuma ya rabu da shi. Nan take yaron ya warke.
19 Sa'an nan almajiran suka zo wurin Yesu a keɓe, suka ce, “Me ya sa mu muka kasa fitar da shi?