22 Yesu ya ce masa, “Ba sau bakwai kawai na ce maka ba, sai dai bakwai har saba'in.
23 “Saboda haka za a misalta Mulkin Sama da wani sarkin da yake so ya yi ƙididdigar dukiyarsa da yake hannun bayinsa.
24 Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wanda yake bi talanti dubu goma bashi.
25 Da yake ya gagara biya, sai ubangidansa ya yi umarni a sayar da shi da mata tasa da 'ya'yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin.
26 Sai bawan ya faɗi a gabansa ya yi masa ladabi, ya ce, ‘Ya ubangida, ka yi mini haƙuri, zan biya ka tsaf.’
27 Saboda tausayin bawan nan ubangidansa ya sake shi, ya yafe masa bashin.
28 Amma wannan bawa, da fitarsa sai ya tarar da wani abokin bautarsa, wanda yake bi dinari ɗari bashi. Ya cafi wuyarsa, ya ce, ‘Biya ni abin da nake binka.’