20 “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da uwa tasa, ka tafi ƙasar Isra'ila, don masu neman ran ɗan yaron sun mutu.”
21 Sai ya tashi, ya ɗauki ɗan yaron da uwa tasa, ya zo ƙasar Isra'ila.
22 Amma da ya ji Arkilayus ya gāji ubansa Hirudus, yana mulkin ƙasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Amma da aka yi masa gargaɗi a mafarki, sai ya ratse zuwa ƙasar Galili.
23 Sai ya je ya zauna a wani gari wai shi Nazarat, domin a cika faɗar annabawa cewa, “Za a kira shi Banazare.”